in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sanda na neman wasu jagororin adawa ruwa a jallo
2018-08-07 19:11:23 cri
'Yan sanda a Zimbabwe, sun ce suna neman wasu jagororin jami'iyyar gamayyar 'yan adawa ta MDC su 9 ruwa a jallo, bisa zargin su da hannu cikin tashin hankalin makon jiya, wanda ya sabbaba kisan mutane a kalla 6 tare da jikkata wasu da dama.

'Yan sandan Zimbabwe sun bayyana hakan ne a Talatar nan, suna masu cewa mutanen da ake nema, suna da ruwa da tsaki wajen kitsa tashin hankalin na birnin Harare, wanda ya biyo bayan bayyana sakamakon babban zaben da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa ya lashe.

Tuni dai aka cafke mutane a kalla 27 bisa wannan lamari, wadanda kuma ake sa ran a Talatar nan za a gurfanar da su gaban kuliya, a wani mataki na neman masu beli. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China