in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a rikicin bayan zaben Zimbabwe ya kai 6
2018-08-03 09:33:10 cri
Hukumomin 'yan sanda sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar rikicin bayan zaben kasar Zimbabwe wanda ya barke a tsakiyar birnin Harare a ranar Larabar data gabata ya karu zuwa mutane 6.

Kakakin hukumar 'yan sandan kasar Charity Charamba ya fadawa taron manema labarai cewa, birnin Harare ya kasance cikin mummunan yanayi na tashin hankali kwana guda bayan da rikici ya barke lamarin da ya yi sanadiyyar rayukan jama'a da barnata dukiyoyi.

Magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC sun yi fito na fito da jami'an tsaro a ranar Laraba, a daidai lokacin da suka fara zanga zangar nuna kin amincewa da jinkirin bayyana sakamakon zaben shugaban kasar, hakan ya sa aka tura jami'an sojoji inda suka bude wuta kan masu boren domin tarwatsa su. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China