in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzania tana cikin shirin ko-ta-kwana bayan sabon rahoton bullar cutar Ebola a DRC
2018-08-11 15:40:11 cri
Ministar lafiyar kasar Tanzaniya Ummy Mwalimu, ta sanar a jiya Juma’a cewa, a yanzu haka kasar ta gabashin Afrika tana zaman shirin ko-ta-kwana bayan samun sabbin rahotannin bullar cutar Ebola a jamhuryar demokaradiyyar Kongo (DRC). “Mutane suna cikin yanayi barazanar kamuwa da cutar Ebola mai saurin kisa, da zarar suka yi mu’amala da mutanen dake makwabciyar kasar DRC," Mwalimu ta bayyana hakan a Dar es Salaam birnin kasuwancin kasar. Ta kara da cewa: “Al’ummar Tanzaniya suna bukatar daukar tsauraran matakai domin kare kansu daga kamuwa da cutar." A cewarta, ma’aikatar lafiyar kasar ta zaburar da jama’a don su zauna cikin shiri, musamman mutane dake rayuwa a yankunan dake makwabtaka da kasashen DRC, Uganda da Rwanda. (Ahmad Fagam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China