in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
DRC ta ayyana kawo karshen cutar Ebola
2018-07-25 09:15:44 cri

Ministan kiwon lafiyar Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) Oly Ilunga ya sanar da kawo karshen cutar Ebola da ta bulla a lardin Ecuador na kasar a hukumance.

Ministan ya sanar da hakan ne jiya Talata, bayan da aka shafe kwanaki 42 ana sanya-ido ba tare da sake samun wani sabon rahoton wanda ya kamu da cutar ba, kamar yadda dokokin kasa da kasa game da harkokin kiwon lafiya suka tanada. Ya kuma yaba da matakan gaggawa da gwamnati da tawagar likitoci daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) da kungiyar na gari na kawo (MSF) suka dauka, na yiwa mutane 3,300 riga kafin cutar a karon farko, bayan da hukumomin Congon suka amince da alluran.

WHO ta ce, kimanin alamomin gargadi 800 da kuma mutane 1,706 da suka yi mu'amula da wadanda suka kamu da cutar aka gano tare da yi musu rijista. A ranar 27 ga watan Yunin wannan shekara ce dai aka kammala aikin gano wadanda suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China