Bayan da aka tabbatar da barkewar cutar Ebolar, hukumar WHO, da asusun tallafawa kananan raya na MDD, da kungiyar AU da sauran hukumomin duniya, da kasar Sin, da kasar Guinea, da sauran kasashen duniya, sun dauki matakai nan da nan don magance yaduwar cutar Ebola kamar yadda aka yi a lokacin yaduwar cutar Ebola a shekarar 2014 zuwa 2016.
Kungiyar AU ta sanar da cewa, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka dake karkashin jagorancinta, ta kaddamar da shirin tinkarar batun cikin gaggawa, da nuna goyon baya ga kasar Congo Kinshasa wajen yaki da kuma magance cutar Ebola, da tura rukunin jami'an ba da jinya da rigakafin cutar Ebolar zuwa kasar Congo Kinshasa.
A kwanakin baya, direktan kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin dake halartar taron kiwon lafiya na duniya da aka gudanar a birnin Geneva Ma Xiaowei, ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai ga halin cutar Ebola da ta barke a kasar Congo Kinshasa, da samar da gudummawa da tura rukunin likitoci zuwa kasar Congo Kinshasa da zarar an bukaci hakan. (Zainab)