in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barazanar Cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta karu zuwa matakin yankin
2018-08-06 10:18:39 cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce sabuwar barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na barazana sosai ga lafiyar al'umma a matakin kasa da ma yanki, sai dai ta ce barazanarta a duniya ba shi da yawa.

A ranar 1 ga watan nan ne Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da sakamakon gwajin farko, ya nuna cewa akwai mutane dake da cutar a arewacin lardin North Kivu dake arewa maso gabashin kasar.

Wannan ya zo ne kimanin mako guda, bayan ma'aikatar lafiya ta kasar, ta ayyana kawo karshen cutar a lardin Equateur dake yammacin kasar.

Yayin da lardin North Kivu ke kan iyaka da kasashen Rwanda da Uganda, WHO ta ce daga cikin abubuwan da ka iya yada cutar cikin kasar da ma yankin, akwai mahadar sufuri tsakanin yankin da aka samu barkewar cutar da sauran sassan kasar da kuma kasashe makwabta.

WHO ta kara da cewa, yayin da yankin da aka samu barkewar cutar ke dauke da 'yan gudun hijira sama da miliyan guda, da matsalolin da kasar ke fuskanta a kai a kai da kuma dadaddiyar matsalar jin kai dake akwai, yanayin tsaro a lardin Kivu ka iya yin tarnaki ga aiwatar da ayyukan tinkarar cutar, a don haka ta ayyana cewa, cutar na barazana ga lafiyar al'umma a matakin kasa da yanki.

Alkaluman da hukumar ta fitar a baya-bayan nan sun nuna cewa, ya zuwa ranar 3 ga watan Agusta, an samu mutane 43 dake dauke da cutar, daga cikinsu, 13 aka tabbatar yayin da ake zargin 30, kuma 33 daga cikinsu sun mutu. Akwai kuma karin wasu mutane 33 da ake zargin sun kamu da ita, inda ake jiran sakamakon gwajin da zai bada tabbaci. Har ila yau, ma'aikatan lafiya 3 sun kamu da cutar, inda 2 daga cikinsu suka mutu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China