Da yake karin haske game da yarjejeniyar, ministan harkokin wajen kasar Sudan Al-Dirdiri Mohamed Ahmed ya ce, Salva Kiir zai ci gaba da zama shugaban kasar Sudan ta kudu har zuwa lokacin mika mulki, yayin da jagoran 'yan adawa Riek Machar zai rike mukamin mataimakin shugaba na daya. Baya ga mataimakan shugaban kasa guda 4 da za a nada daga jam'iyyun siyasu daban-daban.
Haka kuma, majalisar rikon kwaryar kasar za ta kunshi ministoci 35 daga bangaren gwamnati da na 'yan adawa, ciki har da ministoci 20 daga tsagin gwamnati, guda tara daga bangaren jam'iyyar adawa ta SPLM-IO da Machar ke jagoranta.
Yarjejeniyar ta kara da cewa, majalisar dokokin kasar ta wucin gadi ta kunshi mambobi 550, wato 332 daga bangaren gwamnati, sai kuma mambobi 128 daga bangaren jam'iyyar adawa ta SPLM-IO.
A cewar yarjejeniyar, majalisar za ta yi aiki na watanni uku, a kokarin ganin an warware matsalar da bangarorin biyu ke takkadama a kai, idan kuma ta gaza, za a shirya zaben raba gardama kafin karshen matan Maris din shekara mai kamawa.
An kuma amince cewa, za a kafa wata hukuma da za ta warware matsalar kan iyakoki da ma batutuwan da suka shafi wasu jihohin kasar. (Ibrahim Yaya)