Babban magatakardar MDDr ya kara da cewa, masu safarar bil Adama na aikata wannan laifi ba tare da tausayi ba, kuma da dama daga wadanda ake cutarwa, ba sa samun wata kulawa ta musamman.
Ya ce safarar bil Adama na aukuwa ne sakamakon rashin daidaito tsakanin al'umma, da tashe tashen hankula dake aukuwa a kasashe da yankuna daban daban, lamarin dake tauyewa al'ummu da dama hakkokin su na bil Adama.
Kaza lika yara kanana, da matasa, da 'yan ci rani, da bakin haure, su ne ke sahun gaba wajen fadawa tarkon masu fataucin mutane. Yayin da mata da 'yan mata ke fuskantar kaskanci, sakamakon wannan mummunan laifi. Mr Guterres ya ce ana jefa rayuwar mata da dama cikin ayyukan rashin da'a, da karuwanci, da auren dole ta hanyar fataucin mutane. Yayin da a wasu lokuta ake cire sassan jikin mutanen da suka tsinci kan su a hannun masu fataucin bil Adama.
Daga nan sai Mr. Guterres ya bayyana aniyar MDD, game da yaki da masu fataucin mutane, da tabbatar da ana hukunta dukkanin wadanda aka kama suna aikata hakan, tare da tallafar rayuwar wadanda hakan ya shafa. (Saminu Alhassan)