Koda yake Dujarric ya ce, duk da yarjejeniyar da wasu bangarorin na Sudan ta kudu suka cimma a birnin Khartomun na kasar Sudan, har yanzu ba a kai ga warware wasu batutuwa da bangarorin ke kadaddama kansu ba.
Kakakin na MDD ya ce, tawagar MDD dake Sudan ta kudu, za ta ci gaba da sanya-ido kan yadda ake wannan tattaunawa, yayin da a hannu guda kuma bangarorin da abin ya shafa ke kokarin ganin sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa. (Ibrahim Yaya)