Michael Chiengjiek, ministan cikin gidan Sudan ta kudu, ya fadawa 'yan jaridu a Juba cewa, shugaban kasar Salva Kiir ya amince a kafa kwamitin domin binciko hare-haren da aka kaddamar ma'aikatan bada agajin.
Ministan ya ce taron da suka gudanar sun yi Allah wadai da kona helkwatar hukumar ta kasa da kasa dake Maban, a yankin Upper Nile.
A ranar Litinin ne, wasu matasan Maban suka afkawa ma'aikatan agaji da kayayyakin hukumar dake arewa maso yammacin kasar don nuna bacin ransu na rashin aikin yi a yankunan da suke, inda suka yi fito-na-fito da jami'an tsaro.
Hukumar kare hakkin bil adama ta MDD UNHCR da hukumar tallafawa 'yan gudun hijira ta MDDr a Sudan ta kudu sun yi Allah wadai da kaddamar da hare haren. (Ahmad Fagam)