in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kaddamar da hare hare ta sama kan maboyar Boko Haram
2018-08-05 15:43:48 cri
Wasu hare hare na baya bayan nan da sojojin Najeriya suka kaddamar ya lalata maboyar mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, kakakin rundunar sojojin ne ya tabbatar da hakan a jiya Asabar.

Ibikunle Daramola, kakakin sojojin saman Najeriya ya ce, sun yi nasarar kaddamar da hare hare ta sama a yankin Daban Masara dake jahar a ranar Juma'ar da ta gabata, inda suka yi imanin hallaka mayakan 'yan ta'addan masu yawan gaske.

Kakakin ya ce wani jirgin saman sojojin ya samu nasarar jefa boma bomai a yankunan da suke son kai harin, inda suka yi nasarar lalata wurare masu yawa inda mayakan na Boko Haram ke samun mafaka.

Najeriya tana samun gagarumar nasara a yankin da take da kungiyoyin 'yan ta'adda, inda dakarun tsaron kasar suka yi nasarar fatattakar mayakan na Boko Haram daga dajin Sambisa, wanda a baya ya kasance babban sansanin horaswa na mayakan 'yan ta'addan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China