in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 20 a jihar Zamfara
2018-08-05 15:13:14 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe 'yan bindiga guda 20 kana suka saki wadanda suka kai garkuwa da su a jihar Zamfara dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Jami'in watsa labarai na sojojin kasar Kanar Muhammad Dole ya bayyana cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe cewa, sojojin sun yiwa 'yan bindigan kwanton bauna ne, inda suka yi nasarar kashe 20 daga cikinsu, wasu kuma suka arce da raunin harbin bindiga, baya da babura da dama da a kona. Kana sun kwace makamai da albarusai da babura, wayoyin salula da kuma shanu masu tarin yawa.

Ya kara da cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kashe wasu jiga-jigan 'yan bindiga biyu Bello Danboko da Sani Maza a Yanwari kusa da mazabar Yankuzo da kauyen Mai Tukunya kusa da Dansadau dukkansu a jihar ta Zamfara.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta tura jami'an tsaro dubu 1 da suka hada da sojojin sama da na kasa da 'yan sanda da masu tsaron fararen hula, da nufin kawo karshen hare-haren da 'yan bindigar ke kaiwa a kauyuka da garuruwa a jihar ta Zamfara. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China