in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya kori ministan makamashi
2018-08-07 11:09:53 cri
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya sallami ministan makamashin kasar Boakye Agyarko daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba, fadar shugaban kasar ne ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin.

Sanarwar ta ce, shugaban na Ghana ya bukaci Agyarko da ya damka ragamar ofishinsa ga John Peter Amewu, ministan filaye da albarkatun kasa, wanda zai kasance ministan makamashin kasar na wucin gadi, har zuwa lokacin da za'a nada sabon ministan.

Kawo yanzu ba'a bayyana dalilin sallamar mista Agyarko ba.

Sai dai kuma, wasu rahotannin a cikin gidan kasar sun ce sallamar jami'in yana da nasaba da yunkurin da ma'aikatar makamashin kasar ta yi mai cike da sarkakiya na sauya alkaluman yarjejeniyar kwangilar aikin samar da makamashi wanda aka kulla tsakanin tsohuwar gwamnatin kasar Ghana da wani kamfanin hadaddiyar daular larabawa UAE mai sansanoni a Afrika da yankin gabas ta tsakiya (AMERI) a shekarar 2015, wanda ya kai dalar Amurka miliyan 510.

Sabuwar yarjejeniyar za ta tsawaita yarjeneiyar ta shekaru biyar wanda aka kulla da kamfanin na AMERI wanda a halin yanzu yake aikin makamashin na megawati 300MW a kasar ta Ghana zuwa shekaru 15, sannan an kawo sabon kamfanin da zai ci gaba da gudanar da aikin cikin wa'adin da aka kayyade.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China