Fadar shugaban kasar ta bada sanarwar cewa ta dauki wannan mataki ne bayan kammala bincike game da zargin wanda sashen binciken laifuka na hukumar 'yan sandan kasar Ghanan ya gudanar.
Haka zalika an maido shugaban hukumar wasannin kasar Kwadwo Baah-Agyemang wanda aka kora daga mukaminsa, bayan kammala wani bincike wanda yayi sanadiyyar damke wasu 'yan kasar Ghanan kimaini 60, bayan an zargesu da yunkurin shiga kasar Australia da takardun izini na bogi a lokacin gasar wasannin Commonwealth ta bana.
Sakamakon rahoton binciken, wanda aka mikawa shugaban kasar a Juma'ar data gabata wato 6 ga watan Yulin shekarar 2018, ya nuna cewa, ba'a samu wadanda ake zargin da aikata laifin da ake tuhumarsu dashi ba, kamar yadda sanarwar da Eugene Arhin babban daraktan yada labarai na ofishin shugaban kasar ya sanyawa hannu. (Ahmad)