A lokacin da tawagar ke ziyara a kasar Ghana, mataimakin jagoran jam'iyyar New Patriotic ta Ghana, kuma mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia, da shugaban kwamitin jam'iyyar na kasar Ghana Mr. Freddie Blay da kuma John Boadu, babban sakataren jam'iyyar sun gana da madam Xu Lvping, da sauran mambobin tawagar JKS.
Sannan tawagar JKS ta shirya wani taro, inda aka fadakar da Tunanin Xi Jinping, game da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki. A waje daya kuma, bangaren Ghana ya taya murnar cin nasarar shirya wani taron kara wa juna sani, tsakanin manyan jagororin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da na jam'iyyun siyasa na kasa da kasa. Ya kuma bayyana fatansa na karfafa yin musayar ra'ayoyi da fasahohin mulkin kasa, da tafiyar da harkokin siyasa tsakanin jam'iyyun biyu, ta yadda za a iya daga huldar dake tsakanin jam'iyyun siyasar biyu zuwa wani sabon mataki. (Sanusi Chen)