in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana: Kasar za ta kara zurfafa hadin kai da kasar Sin
2018-07-18 11:03:52 cri

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya ce Ghana na sa ran kara zurfafa hadin kai da kasar Sin a fannoni daban-daban, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba.

Akufo-Addo wanda ya jinjinawa ci gaban da bangarorin biyu ke samu ta fuskar bunkasuwar dangantaka da hadin gwiwa tsakaninsu a shekarun baya-baya nan, ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar takardar nadi daga sabon jakadan Sin a kasar Wang Shiting, inda kuma ya yi godiya sosai ga goyon bayan da gwamnati da jama'ar Sin ke ba kasarsa, tare da sa ran halartar taron koli na Beijing, na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika da za a kira a watan Satumban bana.

A nasa bangare kuma, Mista Wang Shiting ya nuna cewa, Sin na farin ciki sosai da yadda shugaba Akufo-Addo ke ba batun raya dangantaka tsakanin kasarsa da Sin muhimmanci, ya kara da cewa, Sin na maraba da Akufo-Addo da ya halaraci taron kolin Sin da Afrika, kuma yana fatan kara hadin kai da Ghana don daga matsayin dangantakar abota tsakaninsu domin amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China