in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na son kara yawan cocoa da take sarrafawa
2018-07-07 16:44:36 cri
Gwamnatin Ghana da abokan huldarta, na daukan matakan da suka dace, na kara yawan cocoa da ake sarrafawa a kasar zuwa kashi 50 cikin dari bisa na jimilar wanda ake samu duk shekara.

Daraktan bincike da bibiya na hukumar kula da noma da sarrafa Cocoa na kasar, Vincent Okyere Akomeah, ya shaidawa manema labarai a gefen taron dandalin tattauna batutuwan da suka shafi Coacoa na Ghana cewa, akwai bukatar tabbatar da ganin an cimma wannan buri a wani mataki na tunkarar sauyin farashi a duniya.

Ya ce a yanzu, sun samar da hukumar tabbatar da sarrafa kayyaki tare da amfani da su a cikin kasar, saboda shugaban kasar da gwamnati, sun fitar da wata manufa, da ta tilasta sarrafa a kalla kaso 50 cikin dari na Cocoan da ake nomawa a kasar.

Ya kara da cewa, Ghana tana sarrafa ton dubu 250 na Cocoa, wanda shi ne kimanin kaso 25 na jimilar abun da ake nomawa a kowacce shekara, yana mai jadadda bukatar daukan kwararan matakan tabbatar da sarrafa kaso 50 cikin dari, wanda ke bukatar samar da ayarin kwararru da za su sanya ido kan aikin.

Har ila yau, jami'in ya ce a wani bangare na matakan tabbatar da dorewar noman Cocoa da cin dukkan gajiyarta, dandalin tattaunawar ya kafa wani kwamitin kwararru da za su wayar da kai game da inganta amfani da Cocoa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China