in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana Akufo-Addo ya samu lambar yabo ta Afrika
2018-08-01 11:08:48 cri
Gidauniyar kiyaye tashoshin ruwa ta Afrika (APA) ta bayar da lambar yabo ta musamman ga shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo bisa namijin kokarin da ya yi wajen zamanintar da tashar ruwan Ghana.

An bayar da lambar yabon ne a lokacin taron kungiyar kula da sha'anin tashoshin ruwa na yammaci da tsakiyar Afrika (PMAWCA) karo na 39, inda aka karrama kokarin da Akufo-Addo ya yi bisa kashin kansa da kuma gwamnatinsa wajen zamanintar da tashar ruwan kasar ta Ghana.

Shugaban gidauniyar, Guy Manouan, ya yabawa Akufo-Addo sakamakon ingantaccen aikin da ya gudanar a tashar ruwan kasar, matakin da ya janyo hankulan 'yan kasuwa a harkokin sufurin teku.

Taron na PMAWCA, wanda ke gudana a kasar Ghana a halin yanzu, ya samu halartar daraktocin kula da tashoshin ruwa na kasashen yammaci da tsakiyar Afrika kimanin 15 da kuma wasu wakilan kungiyoyin tashoshin ruwa na kasa da (IMO) da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kula da tashoshin ruwa.

Daga cikin sauye sauyen da kasar ta yammacin Afrika mai arzikin zinare, cocoa da kuma man fetur ke gudanarwa sun hada da, aiwatar da matakan da suka shafi tantance kayayyaki ta yanar gizo da kuma takaita dokokin da hukumar ta tsara daga 16 zuwa guda 3 kacal.

Haka zalika an samu kyautatuwar al'amurra wajen tantance kayayyaki, da rage kudaden da ake biya, da inganta tsarin tantancewar.

Mataimakin shugaban Ghanan Mahamudu Bawumia shi ne ya karbi lambar yabon a madadin shugaban kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China