in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COMESA na kara sanya ido don kare masu sayayya
2018-08-07 10:51:55 cri

Hukumar sa-ido ta kasuwar bai daya ta kasashen gabashi da kudancin nahiyar Afirka(COMESA) na shirin kara tsaurara matakan sanya ido don kara ba da kariya ga masu sayayya.

Shugaban hukumar George Lipimile ya shaidawa manema labarai a birnin Nairobin kasar Kenya, cewa wasu harkokin cinikayya da kasashen mambobin kungiyar da manyan kamfanoni suka takaita, na ci gaba da karuwa har ma ya kai ga ci da gumin masu sayayya.

Lipimile ya bayyana hakan ne a gefen taron dandalin binciken shekara-shekara na COMESA karo na 5, yana mai cewa, hukumar za ta bullo da wani tsarin bincike abubuwan dake faruwa a zahiri, tare da daukar matakan da suka dace na daidaita yaki da al'adar takara wanda daga karshe za a kai ga samar da kariya ga masu sayayya.

Jami'in ya ce, galibin al'adar takara dake faruwa a kasashe 21 mambobin kungiyar, matakan kariyar cinikayya ne da gwamnatocin kasashen suka bullo da su da nufin kange kamfanoninsu daga shiga takara.

Ya bayyana cewa, a halin yanzu batun ba da kariya ga harkokin cinikayya ya kasance daya daga cikin babbar barazana ga zirga-zirgar kayayyaki da hidimomi a yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China