Vaezi yace, shugaba Donald Trump na Amurka ya gabatarwa Rouhani bukatar ne a lokacin da ya kai ziyara New York don halartar babban taron MDD a watan Satumbar 2017, kamar yadda jaridar Tehran Times daily ta wallafa.
Sai dai bai yi cikakken bayani ba, game da ko Rouhani ya amince da goron gayyatar neman ganawar da Trump ya gabatar masa.
A watan Satumbar shekarar 2013, Rouhani da tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, suka zanta ta wayar tarho a lokacin babban taron MDD karo na 68. Tattaunawar ita ce mafi girma data gudana tsakanin shugabannin kasashen biyu a cikin shekaru sama da 30.