in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kolin Iran ya yi watsi da tattaunawa da Amurka
2018-07-22 20:52:35 cri
Kamfanin dillancin labarai Iran IRNA, ya rawaito shugaban koli na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana cewa, duk wani yunkurin tattaunawa da nufin warware takaddama da kasar Amurka ya kasance a matsayin wani babban kuskure a bayyane karara.

Khamenei ya bayyana a lokacin ganawa da jami'an ma'aikatar harkokin wajen Iran a Tehran babban birnin kasar cewa, kasar Amurka tana yunkurin maido da matsayin da take dashi ne a Iran gabanin juyin juya halin Iran a shekarar 1979, kuma ba zasu taba lamintar hakan ba.

An jiyo Khamenei yana cewa, "dama can Amurka tana da wasu muhimman matsalolin da rashin jituwa tsakaninta da kafuwar jamhuriyar musulunci ta Iran.

Yace rashin amincewar da Amurka ta yi da shirin nukiliyar Iran, da karfin ikon da Iran ke dashi, da kuma irin rawar da Iran din ke takawa a yankin alamu ne a fili dake tabbbatar da adawar da Washington take yi da jamhuriyar musulunci ta Iran.

Bayan matakin da shugaba Trump ya dauka na janye daga yarjejeniyar dakatar da shirin makaman nukiliyar Iran mai cike da tarihi, a ranar 8 ga wata, Amurka ta sake nanata aniyarta na sake kin amincewa da dagewa Iran takunkumin da aka cimma matsaya kansa karkashin yarjejeniyar Iran din, kana Amurka ta sake yin barazanar sanya kafar wando daya da duk wata kasa a duniya data nemi yin huldar ciniki da Iran.

Ita dai Amurka ta janye daga hadaddiyar yarjejeniyar nukiliyar Iran inda ta sha suka daga kasashen duniya. Wasu daga cikin manyan kawayenta na kasashen Turai sun amince zasu cigaba da aiki da yarjejeniyar ta 2015 don gudun kada al'amura su sukurkuce. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China