Gidan talabijin na Press TV ya jiyo Rouhani yana mai cewa, kasar Iran ta kalubalanci shugabannin Amurka inda ta zarge su da nuna rashin dattaku, mugun hali da kuma saba alkawurra daga dukkan fannoni, hakan ya sa Iran ba ta da wani zabi da ya wuce ta yi fito-na-fito da manufofin Amurkar.
Shugaban na Iran ya mayar da martani ne game da kalaman da jami'an Amurkar suka yi na baya bayan nan na dake cewa "babu kanshin gaskiya ko takamammiyar hujja" ya ce wannan wata 'yar karamar barazana ce wadda ba ta da wani tasirin da har za'a mayar mata da martani. (Ahmad Fagam)