Wakilan sun hadu ne a ofishin AU na MDD, domin sauraron bayanai daga mambobin majalisar ta yadda za su samu darasin da za su koya.
AU ce ta bukaci a gudanar da taron a gafen taron manyan jami'ai kan nazarin aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa na MDD a duniya, wanda ke gudana daga ranar 16 zuwa 18 ga watanan da muke ciki a hedkwatar MDD.
Taron na da nufin ba kasashe damar samun darasi daga bayanan da aka samu kamar na nazarin da kasashen mambobin AU suka yi. An bukaci kasashen sun bayyana darussan da suka samu da kuma kyawawan ayyuka da suka yi wadanda suka hada da na kirkire-kirkire da ayyukan masu ruwa da tsaki da na hadin gwiwar da kuma na tabbatar da yadda muradun za su dace da kasashensu. (Fa'iza Mustapha)