An rufe taron yini biyu na shugabannin kungiyar AU karo na 31 a birnin Nouakchott hedkwatar Mauritania. Taro a wannan karo ya ci gaba da babban take na taron da ya gabata wato "Cimma nasarar yaki da cin hanci da karbar rashawa: Hanya mai dorewa wajen canja salon bunkasuwar Afrika ".
Yayin taron, shugabannin Afrika sun tattauna kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda yin kwaskwarima a AU, da dunkulewar Afrika bai daya, da yaki da cin hanci, da ta'addanci, da tsaron shiyyar da dai sauransu. (Amina Xu)