Paul Kagame, wanda kuma shi ne shugaban kasar Rwanda, ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar, a matsayinsa na Wakilin Tarayyar Afrika a wajen taron kolin kungiyar BRICS karo na 10 da ya gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Ya ce ayyukan masana'antu na da ma'ana idan aka hada da sabbin fasahohi. kuma kalubale ga nahiyar Afrika shi ne, tabbatar da wannan yunkuri ya dore ko kuma ya kara samun ingantuwa.
A ranar karshe ta taron na yini 3, shugabannin BRICS sun gayyaci shugabannin Afrika da wasu shugabannin kasashen kungiyar raya yankin Afrika ta Kudu wato SADC, a wani bangare na tattaunawa da wadanda ba za su samu damar halartar taron ba.
An gayyaci Senegal a matsayinta na shugabar hukumar kula da kawancen raya kasashen Afrika wato NEPAD, da kuma Togo a matsayinta na Shugabar kungiyar ECOWAS. Afika ta kudu mai masukin baki, ta kuma gayyaci Uganda a matsayinta na shugabar kungiyar raya gabashin Afrika.
Sauran shugabannin da suka halarci zaman taron na jiya Juma'a sun hada da Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Zambia Edgar Lungu da na Namibia Hage Geingob da kuma shugaban Mozambique Filipe Nyusi. (Fa'iza Mustapha)