Shugaban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce a ranar 24 ga watan Yulin da muke ciki ne, ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar demokiradiyar Congo ta ayyana kawo karshen yaduwar kwayar cutar Ebola a lardin Equatuer, bayan kwararan matakan da mahukunatn kasar suka dauka na dakile yaduwar cutar da ta bullo a yankunan kasar.
Idan ba a manta ba a ranar 8 ga watan Mayun wannan shekara ce, mahukuntan DRC suka sanar da sake bullo cutar a yankin Bikoro health, wanda shi ne na tara da cutar da sake bullo cikin shekaru 40 a kasar.
Sanarwar ta ce, tun kwanaki 42 da suka gabata rabon da a sake samun rahoton wanda ya kamu da kwayar cutar. Bisa dokokin hukumar lafiya ta duniya da ka'idojin lafiya na kasa da kasa, an kawo karshen cutar ke nan a kasar. (Ibrahim)