Da isarsa, Shugaba Xi ya ga irin kaunar da al'umma da Gwamnatin Mauritius ke wa al'ummar Sinawa.
A cewarsa, Kasar Sin da Mauritius sun dade suna hulda ta abota a tsakaninsu, da kuma kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da yankunansu da kuma wadanda suka shafe su.
Da yake masa maraba, Shugaba Jugnauth na Mauritius, ya ce ya ji dadin karbar bakuncin Shugaban kasar Sin, kuma ya na sa ran ganawa da shi a yau Asabar.
Mauritius ce kasa ta karshe da Shugaba Xi Jinping zai je a ziyararsa ta farko tun bayan da aka sake zabarsa ya shugabanci kasar Sin a karo na 2 a cikin watan Maris. Xi Jinping ya kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa da Senegal da Rwanda da Afrika ta kudu, ya kuma halarci taron kolin Kungiyar BRICS karo na 10 da ya gudana a birnin Johannesburg. (Fa'iza Mustapha)