Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS da na wasu kasashe masu tasowa

Yau Juma'a aka shirya taron tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS da na wasu kasuwanni da kasashe masu tasowa a birnin Johanneburg na kasar Afirka ta kudu, inda shugabanni mahalartan taron suka tattauna kan manyan manufofin da suka shafi hadin kan kasa da kasa a fannin ci gaba, da na hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa, sun kuma kai ga cimma ra'ayin bai daya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tare kuma da gabatar da jawabi.
A yayin jawabinsa, shugaba Xi ya nuna cewa, yanzu ana cikin wani lokaci na neman babban ci gaba da samun manyan sauye-sauye, hakan ya sa kasuwanni masu tasowa da kasashe masu tasowa, ke fuskantar dama da kalubale na bai daya. Don haka, yana da muhimmanci a karfafa hadin kai a tsakaninsu.
Shugabannin kasashen BRICS, da shugabanni ko wakilansu, na wasu kasashen da aka gayyata, sun hada da na Angola, Argentina, jamhuriyar demokuradiyyar Kongo, Garbon, Malawi, Senegal, Togo da dai sauransu, da kuma wasu jami'an kungiyoyin nahiyar Afirka. (Bilkisu)