in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sa ido na kasa da kasa sun jinjinawa jawabin da Shugaba Xi ya gabatar yayin taron BRICS
2018-07-28 16:52:07 cri
Malamai da masu sa ido na kasa da kasa, sun jinjinawa jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron kungiyar kasashen BRICS karo na 10 da ya gudana a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu.

Taron na kasashe masu samun saurin ci gaban tattalin arziki da aka fara daga ranar 25 zuwa 27 ga watan nan, ya samu halartar shugabannin kasashe mambobin kungiyar da suka hada da Brazil da Rasha da Indiya da Sin da kuma Afrika ta Kudu, domin tattauna hanyoyin samun ci gaba na bai daya a yayin da ake fuskantar sabbin kalubale a duniya.

Macharia Munene, Shehun Malami a fannin huldar kasa da kasa a jami'ar kasa da kasa ta Kenya, ya ce kudurin da Xi Jinping ya gabatar, na karfafa hadin kai kan tattalin arziki tsakanin kasashe 5 mambobin kungiyar, a fannonin da suka hada da cinikayya da zuba jari da harkokin kudi da tuntubar juna, zai taimaka wajen tsara tattalin arzikin duniya cikin adalci.

Ya ce hadin kai a fanni tsaro, muhimmin bangare ne na kawancen kungiyar, a don haka, kiran da Shugaba Xi ya yi na kara jajircewa, na da muhimmanci gaya ga inganta zaman lafiya a duniya.

A nasa bangaren, babban malami a Jami'ar Limpopo ta Afrika ta kudu Shepherd Mpofu, ya ce kiran da shugaba Xi ya yi na kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa tare da warware rikice-rikice bisa hawa teburin sulhu, abubuwa ne masu karfafa gwiwa, a yayin da ake tsaka da fama da kalubalen tsaro a duniya baki daya.

Ya kara da cewa, samun ci gaba ya dogara ne ga samun ingantaccen tsaro. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China