Da yake tsokaci game da wannan batu, mataimakin shugaban cibiyar sanya ido game da al'amuran da suka jibanci wanzar da zaman lafiya ko JMEC a takaice Augostino Njoroge, ya ce ya kamata kasashen dake shiga tsakani wato Sudan da Uganda, su kara azama wajen kawo karshen batutuwa da ake da sabani a kan su.
Mr. Njoroge ya ce wanzar da zaman lafiya na bukatar manufofi masu dorewa. Don haka ya wajaba a dauki matakan shawo kan kashe kashen rayukan jama'a.
An dai gudanar da zaman na karawa juna sani ne na yini hudu, a birnin Juba, fadar mulkin Sudan ta kudu. Taken taron shi ne "Gaggauta wanzar da zaman lafiya ta hanyar fadakar da matasa game da yanayin da ake ciki a Sudan ta kudu". Ya kuma samu halartar dalibai 200, karkashin lemar shirin wanzar da zaman lafiya da ci gaba na WPDI. (Saminu)