in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori masu adawa da juna a Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniya kan shugabanci da raba iko
2018-07-18 10:29:22 cri
Kasar Sudan, ta ce bangarorin dake rikici a Sudan ta kudu, sun cimma yarjejeniya game da shugabanci da raba iko, wadda za a rattabawa hannu a gobe Alhamis.

Yanzu haka, bangarorin na Sudan ta Kudu dake rikici da juna, na tattaunawa a Khartoum, bayan Gwamnatin Sudan ta shiga tsakani, karkashin umarnin kungiyar raya yankin gabashin Afrika wato IGAD.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sudan da fitar, wadda ta bayyana yarjejeniyar da bangarorin suka cimma, ta ce rattaba hannu kan yarjejeniyar na nufin warware dukkan wasu batutuwan da ake takaddama kansu a Sudan ta Kudu, ta na mai bayyana fatan yarjejeniyar za ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Yarjejeniyar da za a rattabawa hannu, ta kunshi kammala yarjejeniyar zaman lafiya ta Khartoum, wadda bangarorin suka rattabawa hannu a ranar 27 ga watan Yuni, wadda ta yi tanadin tsagaita bude wuta nan take da daukar tsawon kwanaki 120 kafin sauya mulki, inda ta fara aiki nan take a ranar da aka cimmata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China