in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantaka ta yi tsami a tsakanin Sudan ta kudu da wasu kasashen yammacin duniya 4
2018-07-18 10:06:30 cri
An samu tabarbarewar huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sudan ta kudu da wasu kasashen yammacin duniya 4 bayan da a kwanan nan jakadun kasashen suka yi kakkausar suka game da harkokin cikin gidan kasar ta gabashin Afrika.

Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kudun ya zargi kasashen Amurka, Birtaniya, Norway da Faransa, da yin katsalandan kan harkokin cikin gidan kasar bayan da a kwanan nan kasashen masu karfin fada aji na yammacin duniya suka yi Allah wadai da tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasar Sudan ta kudun Salva Kiir na wa'adin mulki karo na uku inda suka bayyana matakin da cewa cigaba da take hakkin bil adama ne.

Baak Valentino Wol, wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta kudu ne ya bayyana cewa, shugabannin kasashen waje ko kuma wakilan gwamnatocin kasashen waje ba su da ikon sukar lamarin majalisar dokokin kasar ko kuma su ce za su shawarci shugaban kasar na cewar ya janye matsayar da majalisar dokokin kasar ta cimma.

A makon da ya gabata ne 'yan majalisar dokokin kasar Sudan ta kudun suka kada kuri'ar amincewa da kara wa'adi na uku na mulkin shugaban kasar, da mataimakansa biyu da gwamnonin jahohi har zuwa watan Yulin shekarar 2021. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China