Tawagar jami'an tsaron tekun masu yaki da bakin haure na birnin Zuwara sun yi nasarar ceto bakin hauren su 27 ne daidai lokacin da suke daf da rasa rayukansu kamar yadda sashen hukumar tsaron na Zuwara ya sanar.
Sanarwar ta ce, bakin hauren da aka ceto sun fito ne daga kasashe da dama daga Afrika da kasashen larabawa, daga cikinsu akwai mata 5 da wata karamar yarinya.
Tuni dai aka samar da tallafin magunguna ga 'yan ciranin, kana hukumomin tsaro na cigaba da bincike a birnin don gano musabbabin da ya haddasa hadarin.
A ranar Laraba, sojojin ruwan kasar Libya sun sanar da cewa sun ceto 'yan cirani kimanin 574 a gabar tekun yammacin kasar a aikin sintirin da suka gudanar sau uku a jere. (Ahmad Fagam)