in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta sanar da dakatar da ayyuka a tashar man fetur dake yammacin kasar
2018-07-18 10:42:41 cri
Hukamar samar da man fetur ta kasar Libya, ta sanar da dakatar da aiki a tashar dako da adana mai ta Zawiya dake yammacin kasar. Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Talata, ta ce hukumar ta dakatar da dakon danyen man fetur a tashar Zawiya daga ranar 16 ga watan nan. Wannan ya biyo bayan raguwar ayyuka a rijiya hakar mai ta sharara, sanadiyyar harin da aka kai mata a baya-bayan nan, tare da sace ma’aikatan kamfanin Akakus 4. Shugaban hukumar, Mustafa Sanalla, ya ce tsaron ma’aikata shi ne abun da suka sanya gaba, kuma al’amarin na bukatar rufe wurin tare da wasu tashoshin. Ya ce za su bada fifiko ga bukatar mai a cikin kasar, sannan a yanzu, duk abun da Sharara ke samarwa zai tafi ne ga matatar mai ta kasar. A ranar Asabar da ta gabata ne wasu tsageru suka sace injiniyoyi 4 da suka hada da ‘yan asalin Libya 3 da ‘dan Romania 1, a yankin hakar mai dake kudancin kasar. Hukumar ta ce an saki biyu daga cikin mutanen 4 jim kadan bayan sace su. Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin sace mutanen. (Fa’iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China