Salame ya bayyana haka ne yayin da yake ba da rahoto ga kwamitin sulhu a jiya Litinin a Tripoli babban birnin kasar, game da halin da Libya ke ciki da yadda ake aiwatar da shirin matakai a Libya da MDD ta gabatar, inda ya kara da cewa, a cikin 'yan watanni na farkon bana, an kwantar da kura a kasar Libya. An kuma shirya zaben kananan hukumomi karkashin goyon bayan MDD, kana an sake kafa ofisoshin MDD a Tripoli da Banghazi, haka zalika an soma yunkurin shawarwari.
Baya ga haka, Salame ya ce, wannan wani muhimmin sashe ne na shirin wanda ya sa jama'ar Libya gaba cikin tsarin siyasar kasar, kuma wannan ne karon farko da suka sa himma wajen shiga yunkurin farfado da tsarin siyasa da shawarwari. (Bilkisu)