in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban hukumar tallafin Islama ta Libya
2018-08-05 16:23:37 cri
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da shugaban hukumar bada tallafi ta kasar Libya a jiya Aasabar a babban birnin kasar Tripoli, jami'an kasar ne suka tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Abbas al-Qadi, shi ne shugaban gudanarwar hukumar tallafi da al'amurran addini na halastacciyar gwamnatin kasar Libya, an yi garkuwa da shi ne da safiyar Asabar kana aka yi awon gaba da shi zuwa wani waje da ba'a tantance shi ba, wani jami'in kasar da ya nemi a sakaye sunansa ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami'in ya kara da cewa, an yi garkuwa da al-Qadi ne a filin jirgin saman Tripoli.

Tun bayan boren shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, kasar Libya ke ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula da tabarbarewar tsaro gami da rarrabuwar kawuna a fagen siyasar kasar.

A kasar Libya, yin garkuwa da mutane ya zama tamkar ruwan dare, inda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka wajen yin garkuwa da ma'aikata baki 'yan kasashen waje da kuma jami'an gwamnati, har ma da fararen hula don neman kudin fansa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China