Gidan talabijin na al-Hadath na kasar, ya ruwaito Fathi al-Majbari ya na sanar da yin murabus daga mukaminsa da kuma Gwamnatin hadin kan kasar, tare da yin kira ga dukkan ministocin da ke kishin kasar su ma su ajiye mukamansu.
Ya ce Tripoli na karkashin ikon 'yan tawaye, kuma sun yi kokarin gyara hakan amman sun gaza, yana mai cewa ba birni ne da ya dace da tsarin siyasa ba, sannan ya na bukatar kulawa sosai.
Ya kara da cewa, gwamnati ta gaza samar da tsaro ga al'ummarta.
Har ila yau, ya ce 'yan tawayen ne ke iko da harkokin kudi, kuma abun dake gudana cikin gwamnatin hadin kan kasar, wasa ne kawai. (Fa'iza Mustapha)