in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Masu halartar gasar wasannin motsa jiki sun hadu da cikas
2018-08-03 09:26:14 cri
Hukumar dake lura da harkokin shige da fice a Najeriya ta ce wasu 'yan wasannin motsa jiki da suka sauka a birnin Ikkon jihar Lagos, domin shiga gasar nahiyar Afirka da za ta gudana a birnin Asaba na jihar Delta, sun gaza cika ka'idojin samun Visar kasar.

Hukumar ta ce 'yan wasa da dama, ba su biya kudaden samun Visar ta yanar gizo kamar yadda doka ta tanada ba. Hakan a cewar ta ya kawo tsaiko ga isar 'yan wasan birnin Asaba, inda sai da ta kai su shafe yini biyu kafin a warware matsalar.

Kimanin 'yan wasa 200 daga kasashe 12 ne wannan matsala ta shafa, duk da cewa gasar za ta gudana ne tsakanin ranekun Laraba zuwa Lahadi.

Dan wasa Timothy Cheruiyot daga kasar Kenya, wanda ya taba lashe lambar azurfa a tseren kasa da kasa na mita 1,500, na cikin wadanda suka hadu da wannan kalubale.

To sai dai hukumar shige da ficen ta Najeriya ta ce daga bisani an shawo kan matsalar da 'yan wsan suka fuskanta. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China