Dan Ali ya bayyana a Abuja babban birnin kasar cewa, an tanadi wata tawagar tsaro ta musamman mai taken "Operation SHARAN DAJI" inda aka tura ta zuwa yankunan dake makwabtaka da jahar Neja domin tabbatar da tsaro a dazukan jahohin arewa maso yammacin kasar da suka kunshin yankunan Zamfara, Sokoto da Birnin-Gwari.
Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar tare da manyan hafsoshin tsaron kasar, wanda ministan tsaron ya ce shi ne batu na baya bayan nan da taron majalisar kasar ya gudanar game da sha'anin tsaro a kasar.
A cewasa, an samar da karin dakarun tsaro na sojoji tare da tallafin jami'an tsaron tattara bayanan sirri, da nau'urorin tattara bayanan sirri karkashin rundunar tsaro ta 207 ta 'yan sandan kasar masu kai daukin gaggawa don wanzar da tsaro a kasar baki daya. (Ahmad Fagam)