Shugaba Putin ya shaidawa manema labarai cewa, shi da Trump suna tattaunawa ta wayar tarho, kana suna ganawa a taruka daban-daban, kuma yanzu lokaci ya yi da za su yi tattaunawa mai zurfi a tsakaninsu da ma batutuwan kasa da kasa na gaggawa. Kuma akwai batutuwa da dama da yanzu haka suke bukatar tattaunawa.
A nasa bangaren shugaba Trump ya ce zai tabo batutuwan cinikayya da soja, makamai masu linzami da nukiliya da ma batun kasar Sin. Ya ce, shi da Putin suna da babbar dama, duba da cewa, kasashen biyu ba sa jituwa a 'yan shekarun da suka gabata. (Ibrahim Yaya)