in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Indonesia ya karu zuwa 82
2018-08-06 10:30:11 cri
Mutane a kalla 82 ne suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sanadiyyar girgizar kasa mai karfin maki 7 da ya lalata dubban gidaje da gine-gine a tsibirin Lombok dake tsakiyar kasar Indonesia.

Kakakin hukumar tunkarar iftila'i ta kasar Sutopo Purwo Nugroho, ya ce Iftila'in ya tilastawa dubban mutane tserewa daga gidajensu, sannan ana aikin kwashe wasu a yankin.

Cikin sakon kar ta kwana da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin ya ce ana duba wadanda suka jikkatan ne a wajen asibitoci, domin asibitocin sun rushe ko kuma suna cikin yanayi mara aminci.

Girgizar kasar ta haifar da fargaba a tsibirin da tsibirin Bali dake makwabtaka da shi da kuma lardin Java dake gabashin kasar, inda mutane ke ta tserewa daga gidajensu da gine-gine.

Wani jami'in hukumar kula da yanayi ta kasar Biana Rahayu, ya ce hukumar ta fitar da gargadi game da aukuwar ambaliyar tsunami, kuma an samu ambaliyar mai tsawon kasa da cintimita 13 a wurare 3 na Tsibirin Lombok.

Ko a ranar 29 ga watan Yuli, kimanin mako guda da ya gabata, an samu girgizar kasa mai karfin maki 6.4 a Tsibirin Lombok, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 17 da jikkatar wasu 3675 tare da raba mutane 8,871 da matsugunansu, baya ga lalata gidaje 14,940. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China