in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka mutu sanadiyar girgizar kasar da ta auku a Mexico ya kai 90
2017-09-11 09:02:56 cri

Mahukunta a kasar Mexico sun tabbatar da cewa, yawan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 8.2 da ta aukawa kasar a daren ranar Alhamis ya karu zuwa 90, baya ga sama da mutane 800,000 da girgizar kasar ta raba da muhallansu. Girgizar kasar ta kuma lalata makarantun gwamnati 324, ciki har da 42 da gine-ginensu suka rushe baki daya.

Zurfin girgizar kasar wadda ta kai kilomita 33, ta mamaye fadin kilomita 96 a kudu maso yammacin garin Pijijiapan a jihar Chiapas, kana ta kada gine-ginen a birnin Mexico, inda aka rika jin karar kararrawar gargadi game da girgizar kasa, lamarin da ya tilastawa mazauna fita kan tituna cikin 'yan mituna kafin tsakiyar dare don tsira da rayukansu.

Bayanai sun kara da cewa, girgizar kasar ta shafi a kalla mutane miliyan 50 a jihohi 12. Ko da yake garin Juchitan dake jihar Oaxaca shi ne garin da wannan bala'i ya fi yiwa barna, inda aka tsamo gawawwakin mutane 36. Jihar Oaxaca dai tana daya daga cikin jihohi uku dake kusa da gabar ruwa wurin da girgizar kasar da fi shafa.

Hukumomi a kasar ta Mexico dai sun bayyana cewa, wannan ita ce girgizar kasa mafi muni da ta taba yiwa kasar barna cikin shekaru 100 da suka gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China