in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 120 sun rasu sakamakon girgizar kasa da ta auku a Mexico
2017-09-20 10:51:23 cri

Da yammacin ranar 19 ga wata, an yi girgizar kasa mai karfin maki 7.1 bisa ma'aunin Richter a jihar Morelos dake yankin cibiyar kasar Mexico. Kuma bisa kididdigar da gwamnatocin jihar suka yi, an ce, a kalla mutane 120 sun rasu sakamakon girgizar kasar.

Bisa labarin da aka samu, an ce, an ji karfin girgizar kasa sosai a birnin Mexico, fadar mulkin kasar, kana an kashe wutar lantarki a wasu yankunan birnin, har an dakatar da tashin jiragen sama a filin jirgin sama na kasar.

Kuma wannan shi ne karo na biyu da aka yi girgizar kasa a kasar ta Mexico cikin makwanni biyu, bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 8.2 a yankin gabar ruwa dake kudancin kasar a ranar 7 ga wannan wata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China