in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta tallafawa kasashen Iran da Iraqi bisa ga girgizar kasar data afka musu
2017-11-14 10:15:56 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce MDDr a shirye take ta kai dauki ga mummunar girgizar kasar data afkawa kasashen Iran da Iraqi.

A wata sanarwa ta bakin kakakin sakataren MDDr Stephane Dujarric ya ce, mista Guterres ya yi matukar kaduwa sakamakon hasarar rayukan da aka samu a girgizar kasar mai karfin maki 7.3 wanda ta afkawa iyakokin kasashen biyu.

Sama da mutane 400 ne suka mutu, kana wasu mutanen 7,000 suka jikkata.

Sanarwar ta ce sakatare janar din ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda ibtila'in ya shafa da gwamnatin kasashen Iran da Iraqi, kana ya yi fatar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.

Sannan ya yabawa kokarin hukumomin bada agaji na cikin gida.

Sanarwar ta ce MDD a shirye take ta tallafawa kasashen biyu.

Wannan ita ce girgizar kasa mafi muni da aka samu a cikin wannan shekara, baya ga wadda ta faru a birnin Mexico a watan Satumba, wadda aka ga alamunta har a kasashen Turkiyya da Pakistan. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China