in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karin kusoshin jam'iyyar APC a Najeriya sun yi sallama da ita
2018-08-02 09:30:17 cri
Wasu karin manyan kusoshin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta 'yan adawa. Hakan dai na zuwa ne gabanin babban zaben kasar dake tafe a farkon shekara mai zuwa.

Cikin wadanda suka sauya shekar a jiya Laraba, hadda gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, da kakakin jam'iyyar ta APC Bolaji Abdullahi. Abdullahi wanda a watan Yunin da ya gabata aka zabe shi a matsayin kakakin jam'iyyar ta APC, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga APC ne, sakamakon yadda a fakaice aka amshe ikon dake tattare da kujerar ta sa, matakin da a cewar sa ya yi hannun riga da sahihin tsarin siyasa.

Shi kuwa gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal bai kai ga fayyace dalilin sa na fita daga jam'iyyar mai mulki ba.

A shekarar 2015, jam'iyyar APC ta yi nasarar amshe mulki daga PDP wadda kafin hakan ke mulkin kasar tsawon shekaru 16 wato tun daga shekarar 1999.

Da ma dai a Najeriyar an saba ganin 'yan siyasa na musayar sheka da zarar manyan zabukan kasa sun matso, kuma ko da a ranar Talata ma shugaban majalissar dattijan Najeriyar Bukola Saraki, ya ayyana fitar sa daga APC. A makon da ya gabata kuma, wasu karin 'yan majalissar dattawa, da na majalissar wakilai, sun fice daga jam'iyyar suka kuma koma jam'iyyar PDP.

Haka zalika wasu 'yan majalissun dokokin jihohin Benue, da Kwara da Sokoto, su ma sun ayyana komawa jam'iyyar PDP, a wani mataki na nuna goyon baya ga gwamnonin jihohin su.

To sai dai kuma a bangaren sa, shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya ce ko alama bai damu da ficewar da wasu 'yan siyasa ke yi daga jam'iyyar APC mai mulki ba, a gabar da wasu ke ganin hakan na iya illata tasirin jam'iyyar. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China