in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta Shirya dakile sake bullar Cutar Ebola a kasar
2018-08-01 20:45:17 cri
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta hannun cibiyar kiwon lafiya dake jihar Ogun ta kaddamar da sabuwar motar daukar marasa lafiya ta gaggawa a iyakar Idi-Iroko don daukar matakin dakile barazanar sake bullar cutar Ebola daga kasashen Laberia da kuma Kongo dake makwabtaka da Najeriya.

An ruwaito cewar za'a yi amfani da motar ce wajen bayar da taimakon gaggawa ta hanyar daukar wadanda ka iya kamuwa da cutar da kuma sauran manyan cututtuka bayan an yi masu gwajin cututtukan.

A lokacin da yake kaddamar da motar Daraktan Cibiyar dake aiki a Ma'aikatar kiwon kafiya ta tarayya Dakta Aled Okoh,ya bayyana cewa motar za ta taimaka sosai wajen gudanar da aikin kuma samar da motar yana daya daga cikin bin umarnin hukumar lafiya ta duniya wajen kare bazuwar cutar zuwa sassan kasar.

Okoh, wanda Mista Taiwo Afolabi wani Shugaban Cibiyar ya wakilce shi a wajen kaddamarwar ya ci gaba da cewa motar za ta kawo sauki wajen kai taimakon gaggawa a iyakar ta Idiroko

Shi ma a nasa jawabin Kwantirolan hukumar hana fasa kwauri dake jihar Ogun Mista Michael Agbara wanda Christiana Adamu ta wakilce shi ya yabawa shirin kuma hakan zai taimaka wajen magance kalubalen kiwon lafiya a iyakar.

Shi ma wani jami'I a cibiyar ta Idi-Iroko Adeniyi Ogungbayi, ya yi nuni da cewa, rashin motar a iyakar a lokacin da cutar ta shigo cikin Nijeriya a shekarar 2014 ya janyo tarniki ga Nijeriya, amma zuwan motar da kuma horas da jami'an kiwon kafiyar da aka yi za su taimaka wajen gudanar da taimakon gaggawa.

A cewar sa, yanzu Kam sun shirya don yakar cutar ta Ebola da kuma sauran manyan cututtuka daka iya kunno kai a iyakar ta Idiroko."

Babban Likita a babban asibitin dake Idiroko Dakta Margaret Kilanko da kuma Sakatare Janar na kungiyar hadakar iyaka da Nijeriya da Benin Dakata Bonny Abisogun-Botoku, sun jinjinawa gwamnatin tarayya a bisa daukar wannan matakin da suka ce zai taimaka wajen magance yaduwar manyan cukuttuka zuwa cikin kasashen biyu.(Leadership A Yau)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China