in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da yunkurin dinke barakar a tsakanin Habasha da Eritrea
2018-07-11 09:41:03 cri
Kwamitin sulhun MDD yana maraba da shawarar da kasashen Habasha da Eritrea suka dauka na kawo karshen yakin da suke gwabzawa da kuma kokarin shimfida zaman lafiya.

Sanarwar da kwamitin ya fitar ta nuna yadda mambobin kwamitin suka yaba da sanya hannun da bangarorin biyu suka yi kan yarjejeniyar zaman lafiya ta hadin gwiwa da kuma karfafa alaka a ranar Litinin da ta gabata, kana MDDr tana maraba da yunkurin da bangarorin suke yi na kokarin maido da huldar diplomasiyya a tsakaninsu da kuma bude sabon babi na hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kasashen.

Sanarwar ta ce wannan wani muhimmin cigaba ne da aka samu a tarihi, kuma gagarumar nasara ce wadda za ta haifar da kyakkyawan sakamako a tsakanin kasashen na gabashinn Afrika har ma fiye. Mambobin kwamitin sulhun MDDr suna maraba da yunkurin Habasha da Eritrea na yin hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin, da cigaban yankin, da dinke baraka da kuma aniyar da Eritrea ta nuna na shiga a dama da ita a harkokin kungiyar raya kasashen shiyyar gabashin Afrika (IGAD).

Ita dai Eritrea ta fice daga kungiyar IGAD ne a shekarar 2007, amma ta sake shiga kungiyar a 2011. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China