in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalissar dattijan Najeriya ya fice daga jam'iyya mai mulki
2018-08-01 11:33:44 cri
Shugaban majalissar dattijan Najeriya Bukola Saraki ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki, amma bai bayyana komawarsa wata jam'iyyar ba tukuna. Hakan na zuwa ne watanni 7 gabanin kada kuri'u a babban zaben kasar na watan Fabarairun badi.

Bukola Saraki ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki ne a jiya Talata ta sakon Twitter da ya wallafa. Tuni dama wasu da ake ganin magoya bayansa ne suka sauya sheka daga jam'iyyar ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Kafin fitarsa, gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara, jihar da Sarakin ya fito ya bayyana komawarsa jam'iyyar PDP. Kaza lika cikin makon da ya gabata, shi ma gwamnan jihar Benue dake tsakiyar Najeriya Sam Ortom ya sauya sheka daga APCn zuwa jam'iyyar PDP. A dai makon jiyan, su ma wasu 'yan majalissun dokokin kasar da dama sun sauya sheka daga APC mai mulki zuwa jam'iyyar PDP ta adawa.

Game da hakan, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ba shi da wata damuwa game da ficewar wadannan 'yan jam'iyya ta APC, musamman ganin yadda wasu ke hasashen cewa hakan na iya haifar masa da matsala, a kudurinsa na neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar a babban zaben na badi.

An dai zabi Saraki a matsayin shugaban majalissar dattijan Najeriya ne a watan Yuni na shekarar 2015 bayan babban zaben. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China