in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna bacin ranta game da sabuwar dokar majalisar dokokin Isra'ila
2018-07-21 15:06:35 cri
A jiya Juma'a, MDD ta bayyana rashin jin dadinta dangane da wata sabuwar doka da majalisar dokokin Isra'ila Knesset ta amince da ita, wadda ta halasta nuna wariya ga Larabawa 'yan tsiraru dake kasar.

Kakakin MDDr Farhan Haq ya bayyana cewa, MDD ta jaddada matsayinta na mutunta ikon kowace kasa a duniya karkashin dokokin kundin tsarin mulkin kasar, sai dai ta jaddada muhimmancin mutunta dokokin da suka shafi hakkin bil adama, ciki har da kare hakkin tsirarun kabilu.

Haq ya fada a taron manema labarai cewa, aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan rikicin dake wanzuwa tsakanin al'ummomin Palastinawa da Isra'ila wanda yayi daidai da yarjejeniyar da aka cimma ta MDD ne kadai hanyar da za ta tabbatar da samun dawwamamman zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu, kuma zai tabbatar da cimma burin al'ummomin bangarorin biyu.

Ya ce "muna yin kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su guji nuna fifiko ga wani bangare guda wanda hakan zai iya gurgunta warware takaddamar dake tsakanin sassan biyu."

A ranar Alhamis ne majalisar dokokin Isra'ila Knesset, ta amince da wata doka mai cike da sarkakiya wadda ta bayyana cewa Isra'ila kasa ce ta Yahudawa kadai. Dokar ta ce Yahudawa ne kadai suke da 'yancin yin walwala a kasar.

Dokar ta kwace matsayin da Larabci ke da shi a matsayin yaren da ake amfani da shi a hukumance inda ta amince da yaren Hebrew kadai. Adadin Larabawa dake kasar ya kai kashi 20 bisa 100 daga cikin adadin yawan jama'ar kasar miliyan 9. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China