Mr. Liu ya bayyana hakan ne, yayin wani zama na karawa juna sani game da yanayin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa, da yadda hakan ke shafar ci gaban mai dorewa, wanda cibiyar raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta MDD (ECOSOC) ta shirya.
Liu ya ce, ci gaban tattalin arziki kadai ba zai wadatar da bukatar al'ummun duniya ta cin gajiyar bai daya ba. Kuma duk da irin fadadar tattalin arziki da ake samu, a hannu guda duniya na fuskantar karin kalubale. Don haka ya dace kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, wajen samar da ci gaba mai dorewa, da aiwatar da manufofin bai daya, karkashin dokoki da aka tsara masu cike da adalci, da daidaito, wadanda kuma za su baiwa kowa damar cin gajiyar kasuwanci tsakanin sassa daban daban.
An dai gudanar da zaman ne na manyan masana harkokin kasuwanci da cinikayya, a hedkwatar MDD dake birnin New York. (Saminu)